Taƙaddama tsakanin Namibiya da Jamus
April 2, 2014Gwamnatin Jamus ta yi watsi da buƙatar da wasu Al'ummomin ƙabilun Namibiya suka yi na ta nemi afuwa a gurinsu saboda cin zarafi da kisan ƙare dangi da Jamus ɗin ta aikata a kan ƙabilu Herero da Nama .
Al'ummar Namibiya na buƙatar Jamus ta nemi afuwa
Namibiya dai ita ce ƙasa ta ƙarshe a Nahiyar Afirka da ta samun yancin kai a shekarun 1990 daga Afrika ta Kudu wacce ta zi mata mulkin mallaka daga shekarun 1915 zuwa 1990.To amma tun can da farko a zamanin dauri a shekarun 1884 Jamus ce uwargijiyar Namibiyar a lokacin ake kiran ƙasar da sunan Afirka ta Kudu maso yammaci. A farkon ƙarni na 19 ƙabilun na Nama da Herero da ke zaune a tsakiyar yankin Cap sun bujerewa 'yan mulkin mallaka a ƙarƘashin jagorancin shugaban ƙabilun Jonker Afrikaner. waɗanda suka kori Jamusawa da ke yankin. abin da ya janyo musu martani mai tsauri abin da ya sa aka kori da dama daga cikin su da ke zaune a yanki na hamada yayin da wasu aka karkashesu kana wasu suka mutu da yuwan da ƙishirwa.
Daga baya dai an yi ƙoƙarin zaƙulo gawarwakin jama'ar da suka mutu a sakamakon wannan al'amarin wanda kuma aka kawosu a nan nahiyar turai domin yin gwaje-gwaje don tantance ƙabilun. Utjiua Muinjangue ita ce shugabar wata ƙungiyar ta Herero Genocid. Ta ce: '' Jamusawa ba sa son wannan magana ta cin zarafi na 'yan ƙabilar Herero da Nama ina tuni a wani lokaci sai da suka ce a daina yin amfani da kalmar kisan ƙare dangi a kan wannan batu. Sannan kuma suka ce a daina maganar; amma a zahiri abin da 'yan mulkin mallakar suka yi wa kakaninmu kisan ƙare dangi ne saboda sun yi wa mata fyaɗe sun azabatar da su sun kashe wasu dubban rayukan.''
Manazarta na tunanin cewar Jamus ba za ta nemi afuwar ba
Manazarta dai na kallon cewar abin da ya faru shi ne irin na gwada ƙasaita ta jinsi ta Turai fiye da ta Afirka a waccan lokaci kuma a yanzu wata dama ce ga Jamus ta tuna baya. Sai dai wani mai yin sharhi a kan al'amuran siyasa Hennig Melber ya ce da wuya Jamus ta nemi Afuwa. Ya ce: ''A hukumance da ka nemi afuwa to ka yarda ka aikata laifi da zaran Jamus ta fito ta nemi afuwar to wannan yana zaman cewar tana da laifi. Shi ya sa a shekarun 2004 a lokacin minstan gwamnatin Jamus da ya hallarci cikon bikin shekaru 100 na lamarin bai nemi afuwa ba.'' Ƙungiyoyi masu fafutuka na ta matsa ƙaimi ga Jamus ɗin da ta amince ta nemi afuwa amma ba tare da samun nasara ba har kawo yanzu.
Wata tawagar dai ta wani ministan Namibiya na al'adu da ta zo nan Jamus ɗin domin sake komawa da ƙasussuwan na matatun, babu wani daga cikin jami'an gwamnatin da ya tarbesu saboda ma kaucewa wannan batu.
Daga ƙasa ya a iza sauraron wannan rahoto
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Eidita : Mohammad Nasiru Awal