1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaitaccen tarihin Goodluck Ebele Jonathan

Ubale MusaMarch 25, 2015

Ɗan shekaru 57 kuma tsohon malamin makaranta shugaban Najeriyar tauraruwarsa ta fara haskakawa a shekarun 1999 a matsayin mataimakin gwamnan jiharsa ta Bayelsa.

https://p.dw.com/p/1ExRJ
Nigerianischer Präsident Goodluck Jonathan 11.11.2014
Hoto: picture-alliance/AP

To sai dai kuma cikin ƙasa da shekaru 11 ya kafa tarihin zama ɗan siyasa na farko da ya kai har ga kujerar shugaban ƙasar ba tare da nuna buƙatarsa a bainar jama'ar ƙasar ba ta Najeriya . A yayin da a cikin watan Mayun shekara ta 2010 ya gaji tsohon maigidansa Umar Musa Yar'adua wanda Allah ya karɓi ransa kan kujerar shugaban ƙasar.

Zaɓensa a matsayin shugaban ƙasa a shekarun 2011

A cikin watan Aprilun shekara ta 2011 aka zaɓeshi a matsayin shugaban ƙasa.To sai dai kuma ƙasa da tsawon wattani shidda da hawansa kan gadon sarautar ƙasar ta Najeriya dai ne shugaban ya fara ɗanɗana dacin mulkin sakamakon wani harin bam ɗin da ya dakushe bikin cikar ƙasar ta Najeriya shekaru 50 na yancin kai.Abin kuma da har ila yau ya buɗe sabon babin rikici da ma ƙaddamar da boma- bomai cikin ƙasar da ta kalli tada hankali iri-iri a cikin shekaru huɗu na gwamnatin ta Jonathan ga kaɗan daga cikin jawabinsa.

Wahlkampf in Nigeria 2015 Goodluck Jonathan
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

''Samari da 'yan matanmu da dama sun shiga hannu na 'yan ta'adda da suka haɗa da ya'yanmu da ke Chibok. Tabbas za mu ceto 'yan matar mu kuma tabbas za mu ga ƙarshe na ta'addanci. Za mu samar da ƙari na makamai ga sojojinmu, za mu kuma tura runduna ta musamman domin tinkarar 'yan ta'adda da kawo ƙarshen wannan yaƙi da babu hankali a cikinsa.''

Rigingimun da ya fuskanta a tsawon mulkinsa

To sai dai kuma shugaban yana shirin ƙare wa'adin na shekara huɗu ba tare da alƙawarin nasa ya tabbata cikin ƙasar da hakuri ke ƙarewa a cikin sauri.Saɓanin sa'a da rashin takalmin da ya ba shi kaso 58.9 cikin ɗari na sakamakon zaɓen ƙasar na shekara ta 2011 dai, ko bayan shirgin rashin tsaron da ya kai ga shugaban asarar aƙalla ƙananan hukumomi 30 cikin 774 ga Abubakar Shekau da ke ikirarin daula yanzu. Jonathan ɗin har ila yau na shirin tinkarar zaɓɓɓukan ƙasar ne tare da zargin kauda kai ga halin ɓera da rashin iya siyasar da ta kai ga jam'iyyarsa asarar gwamnoninta biyar sannan ga koma bayan na tattalin arzikin ƙasar ya samu. Ga kuma abin da yake bayyanawa

Goodluck Jonathan Wahlen in Nigeria
Hoto: AP

“ Bari na tabbatar muku cewar ƙarƙashin shugabanci na Jonathan ra'ayinku mai daci ba zai kai ga tura ku gidan yari balle sa ku gudun hijira. Na gamsu cewar na cika alƙawari na da ku 'yan Najeriya, kuma yanzu lokaci ne na tunani na gaba, kuma da goyon bayanku mun cimma da dama a shekaru uku da rabi. To sai dai kuma ora asar a kan gaba na buatar arin aiki sossai”

Abin jira a gani dai na zaman sabbabi na dabaru na shugaban da ke da fatan burge 'yan ƙasa da ma sake yin mulki a gaba.