Iran: Dakatar da yarjejeniyar nukiliya
May 15, 2019Talla
Iran ta yanke hukuncin yin hakan ne bisa umarnin kwamitin tsaro na kasar kamar yadda ta shedawa kamfanin dillancin labaran kasar ISNA. Wannan na nufin ba lallai ba ne ta ci gaba da takaita harkokinta na makamashin uranium, wanda ake anfani da shi wajen samar da makaman nukiliya da kwararru a duniya ke saka wa ido.
Amincewa da takaita harkokin makamshinta na uranium din bayan cimma yarjejeniyar, ya sanya an dage mata takunkumai. Babu martani daga kasashen Jamus da Britaniya da Rasha da Chaina da kuma Faransa da suka rage cikin yarjejeniyar da aka cimma a shekarar 2015, tun bayan fitar da wannan sanarwar da Tehran din ta yi.