Time: Merkel ce gwarzuwar shekarar 2015
December 9, 2015Mujallar Time ta zabi shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel a matsayin gwarzuwar wannan shekara ta 2015, sakamakon rawar da ta taka a matsalar tattalin arzikin girka da kuma karbar 'yan gudun hijiran Syriya. Sannan kuma mujallar ta yaba gudunmawar da Merkel ta bada wajen daidaita tattalin arzikin kasashen Turai bayan da suka fuskanci matsalar komabayan tattalin arziki
A dangane da haka ne ma mataimakiyar Editan mujallar Time Radhika Jones ke ganin cancanci wannan karramawa.
"Gwarzuwar shekara ta 2015, Angela Merkel ta taka rawar gani a kasashen Turai, musamman wajen ceto tattalin arzikin wasu kasashen Turai dama batun bude iyayokin kasarta ga dubban 'yan gudun hijiran Syriya da ke neman mafaka a kasar a Jamus. Muna ganin wcewar adannan kudurori nata sun dauki hankalin duniya baki daya a baya-bayannan."
Ita dai Merkel mai shekaru 61 a duniya ta kasance mace ta hudu da mujallar Time ta taba zaba a matsayin gwarzon shekara, baya ga sarauniyar Ingila Elisabeth da kuma tsaohuwar shugabar Philippines Corazon Aquina.