Togo: An kashe mutane biyar
October 19, 2017Talla
Uku daga cikin mutanen biyar sun mutu ne sakamakon harbinsu da bindiga a birnin Sokode birni na biyu mafi girma a kasar a cewar ministan yayin wani taron manema labarai da ya jagoranta. Ministan tsaron na Togo ya kara da cewa wani kuma daga cikin masu zanga-zangar ya mutu a Lome babban birnin kasar, sai dai kuma 'yan adawar sun ce mutun biyu ne suka mutu a birnin na Lome kadai cikinsu kuwa har da wani yaro dan shekara 11 da haihuwa. Masu zanga-zangar dai sun kafa shingaye a titunan biranen kasar, inda suka sha alwashin cigaba da zanga-zangar har sai sun ga bayan mulkin gado na iyallan gidan Gnassingbe, ko kuma a dawo da kudin tsarin mulkin kasar na 1992.