1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: 'Yan adawa na matsa kaimi

Blaise Dariustone SB
October 4, 2017

'Yan adawar kasar Togo sun sake kira ga magoya bayansu ga yin wata sabuwar zanga-zanga don tilasta wa gwamnatin yin sauye-sauye a kan kundin tsarin mulki domin hana shugaba Faure Gnassingbe yin tazarce.

https://p.dw.com/p/2lCJ5
Togo Demonstration Togo
Hoto: picture-alliance/dpa/A.Obafemi

Tun yau da 'yan kwanki ne dai kasar Togo ke fuskantar matsaloli a game da rikicin siyasa. Sai dai bisa wasu dalillai na cewar rikici ne na cikin gida, kasashe makwabtan kasar sun ja bakinsu sun yi gum dangane da abubuwan da ke wakana a wannan kasa ta yammacin Afirka. Alhaji Yahaya Namassa Kane Daraktan kula da matsaloli na tsakanin iyakokin kasa da kasa na Jamhuriyar Nijar na ganin cewar lalle ne yana da kyau makwabta su sa baki amma kuma batu ne mai sarkakiya. ''Yan adawan kasar ta Togo dai na bukatar ganin an sake dawowa ga kundin tsarin muki na 1992 wanda ya kayade wa'adin mulkin shugaban kasa, batun da bangaran masu mulkin bai amince ba.''

Belgien Togo Protest
Hoto: DW/J. C. Abalo

Sai dai a cewar Mathias Houkpé wani masanin harkokin siyasa na kasar Benin mai makwabtaka da kasar ta Togo ya ce  ko su wadanan kungiyoyi irin su ECOWAS suna da matsala na shiga tsakani a irin wannan yanayi na Togo. "Kugiyoyi na yammacin Afirka irin su ECOWAS abin na da sarkakiya a gare su saboda matsalar ta kai cewar ana neman shugaba mai ci ya yi murabus, sai dai duk da haka ina tsammanin akwai tattaunawa da ake yi ta kasa, domin samun mafita.'' A halin yanzu dai kallo ya koma ga wannan sabon kira da 'yan adawar kasar ta Togo suka yi na zanga-zanga a fadin kasar, da kuma irin martanin da gwamnatin kasar za ta mayar kan wannan mataki.