Yunkurin canza kudin tsarin mulki a Afirka ta Tsakiya
July 14, 2023Sashe na 183 na daftarin sabon kundin tsarin mulkin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ya bayyana cewar 'yan asalin kasar ne kawai za su iya tsayawa takara a zabukan kasa. Wannan yana nufin cewa ba za a dama da duk dan siyasa da ke rike da fasfo na wasu kasashe na yammacin duniya ko kuma na kasar daya daga cikin iyayensa zabe na gaba ba. Tuni ma dai wadanda wannan dokar za ta dakushe fatansu na shugabanci irin su Jean-Pierre Mara, tsohon mataimakin kakakin majalisar dokoki ta shida kuma dan hamayya ya yi tir da wannan tanadi, yana mai cewa zai mayar da 'yan Afirka ta tsakiya masu kasa biyu saniyar ware a zabuka masu zuwa. " Gaskiya ne cewa duk wani kundin tsarin mulki za a iya yi masa gyaran fuska, ma'ana kowane al'umma na iya sake rubuta kundin tsarin mulkin kasarsu. Amma abin da ke faruwa yanzu haka cin mutuncin ne ga al'ummar Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Shugaba Touadéra yana yakar al'ummar Afirka ta Tsakiya ne saboda yawancin shugabannin 'yan adawa suna da fasfo biyu kuma ba su zabi zama 'yan kasa biyu ba, suna da kasa biyu saboda an haife su ne karkashin kasa mai suna Oubangui Chari, lokacin kuma Oubangui Chari na karkashim kasar Faransa ne.
Kwaskware dokar 2015 domin ba da dama ga Touadera ya yi takara a wa'adi na uku a zaben 2025
Wasu masana harkokin siyasa da dokokin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun danganta tanadin da son rai daga shugaban kasa Archange Touadera domin hana duk wadanda za su iya kayar da shi a zaben 2025 tsayawa takara idean aka amince da kundin tsarin mulkin. Ko da Désiré Dominique Erenon, farfesa a fannin shari'a kuma masanin tsarin mulki ya ce bai kamata ma a tayar da jijiyoyin wuya a kan takarar masu fasfo biyu saboda abu ne da aka saje da shi a kasar, inda akasarin mambobin gwamnati ma ke cikin wannan hal "Ba a taba samun matsala a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya game da takarar masu kasa biyu ba. Dalili a nan shi ne, kakakin majalisar dokoki na kasar ma na rike da fasfo biyu: daya na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya daya kuna na Faransa. Akwai ministoci da yawa a gwamnatin Touadéra da suka kasance 'yan kasa biyu,akwai 'yan majalisa da ke riked a fasfo biyu da ke cikin jam'iyyarsa ta siyasa." Sai dai minista Serge Ghislain Djorie na watsa labarai a Jamhuriyar Afirka ta tsakiya kuma mai magana da yawun gwamnati ya ce bai fahimci dalilin da ya sa 'yan adawa ke gutsiri tsomi game da sabbin sharudan tsayawa takarar ba. A gare shi dai, daftarin kundin tsarin mulkin ya ba da damar fayyace dan duma da kabewa da nufin kare muradun 'yan Afirka ta Tsakiya. "Idan ‘yan adawa suna tada hankali don yin Allah wadai da sashen doka da ke bai wa al'ummar Afirka ta Tsakiya damar shiga harkar zabe ko kuma tsayawa takarar shugaban kasa, ina ganin abu ne da ya kamata ya haifar da tambayoyi. Ni, da kai na ga misali, ni dan Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne, mahaifina tun ma kafin shekarar samun 'yancin kai a 1960, dan asalin Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya ne, zan iya tabbatar da hakan. Ba shi da wata kasa face Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Dokokin a bayyane suke, bai kamata mu sake tafka sabuwar muhawara a kan wannan ba, batu ne na makomar al’ummarmu da hukumomi da ya kamata mu tanadar ma wadanda za su gajemu."
Zaben raba gardamar na 30 ga watan Yuli zai bude kofa ga yin tazarce na Touadera
A ranar 30 ga watan Yuli ne aka shirya kada kuri'ar amincewa ko waci da sabon kundin tsarin mulkin kasar a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, wanda ke bude wa Shugaba Toudera babin yin tazarci kamar sauran takwarorinsa na yankin tsakiyar Afirka irin su Paul Biya na Kamaru da Ali Bongo Ondimba ba Gabon da Sassou Nguesso na Kwango Brazaville da Obiang Nguema na Equatorial Guinea.