Ta'addanci na da alaka da cin-hanci
December 15, 2022Cin-hanci da karbar rashawa na zaman wata annoba a cikin al'umma, abin da kungiyar ta Transparency International ta ce yana da tasiri sosai wajen kara hura wutar ta'adanci ta la'akari da yadda wasu daga cikin miyagu ke amfani da talaucin da ke addabar mata da matasa. A hannu guda kuma ana samun cin-hancin a bangaren shari'a da wasu abubuwan da suka yi kama da hakan a rukunin jami'an tsaro, musamman na kan hanya da ke karbar na goro ba tare da sun binciki ababen hawa ba.
Wannan ne ya sanya kungiyar ta Transparency International kaddamar da wani rangadi a wasu yankunan Jamhuriyar ta Nijar musamman a Tahoua da Agadez, a wani mataki na kawo gudunmawa a fafutukar da hukumomin kasar ke yi na dakile cin-hanci da rashawar. An dai tara matasa da kungiyoyin mata da na malamai da wakilan sarakunan gargajiya da jami'an tsaro da 'yan siyasa, wadanda ake ganin za su iya taka rawa cikin al'umma domin fadakar da su kana wannan lamari. Koda yake kungiyoyin sufuri da na direbobi sun sha kai kokensu gurin gwamnati, domin rage musu shingayen binciken ababen hawa a kan hanyoyi. A duk lokacin da ake maganar cin-hanci da rashawa dai, jama'a sun fi nuna yatsa ga 'yan siyasa.