1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Trump alkhairi ne ga Gabas ta Tsakiya- Sharaa

January 21, 2025

Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Ahmed al-Sharaa ya ce babu shakka gwamnatin Trump za ta taimaka wajen wanzar da zaman lafiya a yankin Gabas ta Tsakiya.

https://p.dw.com/p/4pPOO
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Ahmad al-Sharaa
Shugaban gwamnatin rikon kwarya na kasar Siriya Ahmad al-SharaaHoto: Giuseppe Lami/ANSA/picture alliance

A wata sanarwa da hukumomin Siriyan suka fitar sun bayyana Trump a matsayin limamin canji wanda zai tabbatar da dorewar zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin Gabas ta Tsakiya baki daya.

Karin bayani: Jagoran Siriya ya gana a karon farko da Amurka 

Kungiyoyin 'yan tawayen da Sharaa ya jagoranta wanda suka  hambarar da gwamnatin Bashar al-Assad a 8 ga watan Disambar 2024, na ta fadi-tashin samun tallafin kudade domin sake gina kasar ta Siriya wacce ta shafe shekaru kusan 13 tana fama da yaki.

Karin bayani: Ko sabbin shugabanin Siriya za su yi dimukaradiyya? 

Amurka da sauran kasashen yammacin duniya sun bukaci sabuwar gwamnatin rikon kwaryar da ta yi duk mai yiwuwa wajen kakkabe masu tsattsauran ra'ayi da kuma yaki da ta'addanci domin ta kasance abokiyar tafiya ga kasashen yamma.