Muhawarar karshe gabanin zaben Amirka
October 23, 2020Talla
A muhawarar Joe Biden ya dora alhakin asarar rayukan da aka samu a game da cutar coronavirus da kakausar suka kacokam a kan shugaba Trump a wani abin da ya kira sakaci da rayukan alumma, ya kuma ce bai kamata ya sake komawa wannan kujera ta shuigabancin Amirka ba.
A daya bangare Donald Trump ya caccaki abokin hamayar sa ne da cewar zai boye a karkashin inuwar dokar Corona ya lalata tattalin arzikin kasar.
Rahotanni dai sun nuna cewar a wannan karon muhawarar ta gudana ne cikin natsuwa ba kamar a lokacin baya ba.