1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump kalubale ne ga Turai - Hollande

Ahmed Salisu
January 27, 2017

Shugaban Faransa Francois Hollande ya bayyana a wannan Juma'ar cewar gwamnatin Amirka da Donald Trump ke jagoranta babbar barazana ce ga kasashen da ke nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/2WVeJ
Donald Trump
Hoto: picture alliance/AP Images/M. Rourke

Hollande ya ce magana ta gaskiya akwai barazana da damar gaske musamman ga batun kasuwanci da ma batun yunkurin da Turai ke yi na ganin a wanzar da zaman lafiya a sassan duniya daban-daban don haka dole ne mu zauna da shi don tattaunawa. Shugaban na Faransa na wadannan kalamai ne lokacin da ya yi wani jawabi ga manema labarai tare da shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel wadda ta ce lokaci ya yi da za su tinkari wannan kalubale da ya kunno musu kai. Wannan dai na zuwa ne bayan da Shugaban Trump ya bayyana cewar zai kawar da shirin nan na cinikayya tsakanin kasarsa da kuma kasashen Turai wadanda suka jima suna dasawa.