Trump na barazana ga yarjejeniyar nukiliyar Iran
April 25, 2018Trump dai ya bayyana yarjejeniyar da kasashen Amirkan da Birtaniya da China da Faransa da Rasha da kuma Jamus suka cimma dangane da batun makamashin nukiliyar Iran din, da yarjejeniya mafi muni da aka taba cimma a duniya, baya ga barazanar janye kasarsa daga yarjejniyar da ya yi ta hanyar kakakabawa Iraan din sabbin takunkumi a watan Mayu mai zuwa. Tuni dai shugaban kasar ta Iran Hassan Rohani ya sanya kafa ya yi fatali da batun yin matsin lamba daga kasashen Amirka da Faransa na sake zama kan tebur domin tattauna sabuwar yarjejeniyar kasa da kasa kan makamashin nukiliyar kasarsa. Trump dai ya bukaci kasashen Turai da su sanya tsauraran matakai ga Iran kafin cimma sabuwar yarjejeniyar, wacce ya ce ita ce za ta maye gurbin ta 2015 din da aka cimma.