1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump na son Rasha ta daina taimakon Siriya

Ramatu Garba Baba
February 17, 2020

Shugaban Amurka Donald Trump ya yi kira ga gwamnatin kasar Rasha da ta janye goyon bayan da ta ke bai wa rundunar gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad na Siriya da ke yakar 'yan tawaye a yankin Idlib.

https://p.dw.com/p/3XsLi
Russland Wladimir Putin & Baschar al-Assad in Sotschi
Hoto: picture-alliance/dpa/Sputnik/M. Klimentyev

A nata bangaren ma, gwamnatin Turkiyya ta nemi Rashan da ta janye goyon bayanta inda ta bayyana damuwa kan rincabewar rikicin yankin na Idlib. Rikicin na baya-bayan da ya yi sanadiyar rasuwar mutane da dama kana ya tilasta wa mutum kusan dubu dari takwas tserewa daga gidajensu, a kaura mafi muni tun bayan barkewar yakin basasa a kasar. 

Dakarun gwamnatin Siriya na kokarin sake kame yankin na Idlib ne da zummar karbe ikonsa daga hannun babbar kungiyar masu tayar da kayar baya da ke da alaka da kungiyar al-Qaeda.