1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka za ta dauki mataki kan Iran

Lateefa Mustapha Ja'afar
August 16, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya sha alwashin daukar tsattsauran mataki domin tabbatar da ganin an sake kakabawa Iran duk wasu takunkumai na Majalisar Dinkin Duniya da aka dage mata da murya guda a majalisar.

https://p.dw.com/p/3h286
USA | US-Präsident Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Walsh

Shugaba Donald Trump ya bayyana hakan ne, biyo bayan watsi da bukatar Amirkan da Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi, dangane da sanya wa Iran takunkumi na har abada kan makamai. Trump ya bayyana cewa a jira shi nan da mako mai zuwa domin ganin irin matakin da zai dauka.

Trump dai zai yi amfani ne da takaddamar da ake fama da ita kan cewa har yanzu Amirkan na cikin yarejeniyar nukiliyar Iran din da ya ayyana ficewa a baya. Matakin da Trump din ya ce zai dauka da ake  kira da "Snapback" da Turancin Ingilishi dai, ya bai wa kasashen da ke cikin yarjejeniyar damar mayar da takunkuman da aka dagewa Iran din bayan cimma yarjejeniyar nukiliyarta a shekara ta 2015, in har ta saba ka'idojin da suka cimma.