SiyasaAmurka
Trump ya daukaka kara zuwa kotun koli
January 4, 2024Talla
Jihar Colorado ita ce ta farko da ta yanke hukuncin haramta wa Trumptakara bisa tuhumarsa da tunzura afka wa majalisar dokokin Amurka a ranar 6 ga watan Janairun 2021.
Trump wanda ke kan gaba a cikin 'yan takarar neman shugabancin kasar Amurka na 2024 a Jam'iyyar republican yana bukatar kotun kolin ta sake duba hukuncin.
Karin Bayani: Trump: Ni ake hari a binciken Capitol
Manazarta dai na ganin karar za ta jefa kotun kolin cikin wadi mai sarkakakiya na siyasa.
Uku daga cikin alkalan kotun dai Trump ne ya nada su a lokacin da ya ke shugaban kasa.