1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amirka ta janye sojojinta daga Siriya

Lateefa Mustapha Ja'afar AH
December 20, 2018

Wannan sanarwa ta bazata dai ta fito ne cikin wani faifen bidiyo da fadar White House ta wallafa. Sai dai matakin na Trump ya janyo suka daga bangarori da dama ciki kuwa har da ma'aikatar tsaron Amirkan ta Pentagon.

https://p.dw.com/p/3ARAv
Syrien Manbidsch US Patrouille
Hoto: picture-alliance/AP Photo/H. Malla

Shugaban na Amirka Donald Trump dai ya wallafa a shafinsa na Twitter cewar: "Mun cimma nasara a kan 'yan IS a Siriya, shi ne dalilin da ya sanya muka kasance a Siriya." A yayin da yake karin haske kan batun janye sojojin Amirkan daga Siriya kuwa, Trump cewa ya yi lokaci ya yi da ya kamata su fice, kana dakarunsu su koma gida.

Washington Trump Treffen mit Demokraten zu Haushaltssperre
Hoto: picture-alliance/EPA/MediaPunch

Sai dai jim kadan bayan wannan jawabin nasa, 'yan majalisun dokokin kasar daga bangaren adawa da ma jam'iyyarsa ta Republican da ke mulki, sun nuna rashin jin dadinsu kan daukar matakin gaban kai da Donald Trump din ya yi wajen yanke hukuncin da suke wa kallon danye da ke barazana ga tsaron kasarsu. Tuni dai shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya yaba da matakin na Amirka na janye dakarun nata daga Siriyan. Putin ya bayyana hakan ne a yayin taron manema labarai na shekara-shekara da ya saba gabatarwa duk karshen shekara.