1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya katse kudaden raya kasa ga Siriya

Yusuf Bala Nayaya
March 31, 2018

Shugaban ya ba da umarnin tsayar da biyan kudaden ne take bayan rahoton fitar wasu karin makudan kudade zuwa kasar ta Siriya da yaki ya daidaita.

https://p.dw.com/p/2vHXt
USA | Trump kündigt militärischen Rückzug aus Syrien an
Hoto: Getty Images/J. Swensen

Shugaba Donald Trump na Amirka ya ba da umarni na a dakatar da kudi sama da dala miliyan 200 da kasar ta bayyana za a yi amfani da su wajen ganin an farfado da Siriya ta hanyar aikace-aikace na samar da wutar lantarki da ruwan sha da hanyoyi. Mujallar Wall Street ta ba da wannan rahoto a ranar Juma'a.

Shugaban ya ba da umarnin tsayar da biyan kudaden ne bayan rahoton fitar wasu karin makudan kudade zuwa kasar ta Siriya da yaki ya daidaita. Mahukuntan na birnin Washington dai ya bayyana daukar wannan mataki da dalilai na sake nazarin rawar da kasar ta Amirka ke takawa a kasar ta Siriya da ta dauki shekaru bakwai ana fafata yaki.