1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Soke duk wata tattaunawa da 'yan kungiyar Taliban

Abdoulaye Mamane Amadou
September 10, 2019

Shugaban Amirka Donald Trump ya tabbatar da cewa bakin alkalami ya riga ya bushe dangane da duk wata tattaunawa tsakanin kasar Amirka da kungiyar 'yan Taliban, kwana daya bayan soke wata ganawar sirri a Camp David.

https://p.dw.com/p/3PK4O
Donald Trump
Hoto: Getty Images

Bayan soke batun tattaunawar da ke dab da cimma wata yarjejeniya tsakanin Amirka da kungiyar Taliban da ta shafe shekaru 18 tana gwagwarmaya da makamai a Afganistan, Shugaba Trump ya ce dakarun Amirka da ke Afganistan sun kara matsa kaimi ga mayakan kungiyar tun bayan kaddamar da wani harin da ta kai a birnin Kabul da ya yi sanadiyar rasuwar mutane 12 ciki kuwa har da wani sojan Amirka guda.