Trump ya yi alkawarin kawo karshen rigingimun kasa da kasa
July 19, 2024Donald Trump ya amince da zabensa a matsayin dan takarar shugaban Amurka na jam'iyyar Republican a hukumace, a yayin jawabin da ya gabatar a babban taron jam'iyyar kwanaki kalilan bayan ya tsallake rijiya da baya a wani yunkuri na hallaka shi.
Cikin jawabin na sa tsohon shugaban na Amurkan Trump ya sake jaddada bukatar magance rashin jituwa da rarrabuwar kawuna a tsakanin al'ummar Amurkan.
Ya kara da cewa "Ina neman zama shugaban kasa gadaukacin Amurka, ba rabin Amurka ba, domin babu wata nasara da za a samu na lashe rabin Amurka."
A cikin jawabinsa na mintuna 90, wanda shi ne kololuwar taron jam'iyyar Republikan na kwanaki hudu,Trumpya yi alkawura daban-daban ga masu kada kuri'u ciki har da kawo karshen rikice-rikicen kasa da kasa, da aiwatar da aikin korar baki mafi girma a tarihin Amurka.