1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya yi barazanar murkushe Iran

Abdul-raheem Hassan MNA
May 20, 2019

Shugaban Amirka ya ce idan kasar Iran ta kuskura ta nemi tada rikici da ita ko daya daga cikin kawayenta to ta yi kuka da kanta, domin kuwa a shirye Amirka take ta ga bayanta.

https://p.dw.com/p/3IlEf
Bildkombo - Trump und Rohani

Shugaba Donlad Trump ya yi gargadi da kakkausar murya na murkushe kasar Iran muddin ta yi yunkurin kai wa Amirka da kawayenta hari a wannan lokaci, a wani sakon twitter da Trump ya wallafa na cewa "Idan Iran na son fada, to karshenta ya zo a hukumance. Ba a takalar Amirka."

Barazanar ta Trump ga Iran dai na zuwa ne kwanaki kalilan bayan da shugaban na Amirka ya nuna alamun shiga tattaunawa da gwamnatin Tehran domin kawo karshen tsamain dangantaka tsakanin kasashen biyu.

Amma da alama tsugune ba ta kare ba ganin yadda Amirkar ke kara tura kayan yaki yankin, tare da janye jami'anta daga Iraki kan zargin harin daga magoya bayan Iran.