1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump zai baiyana matakinsa kan nukiliyar Iran

Ramatu Garba Baba MNA
May 8, 2018

Al'ummar duniya sun kasa kunne don jin matakin da Shugaba Donald Trump na Amirka zai dauka a wannan Talata game da yarjejeniyar nukiliyar Iran da kasar da wasu kasashen duniya suka rattabawa hannu a baya.

https://p.dw.com/p/2xL7W
USA PK Präsident Trump über Atomabkommen mit Iran
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Trump ya tsayar da ranar takwas ga watan Mayu a matsayin ranar da zai baiyana wa duniya matakinsa kan batun da ya tayar da hankula da ma janyo musayar zafafan kalamai a tsakaninsa da gwamnatin Iran.

Ba tun yau ba shugaban ke barazanar janyewa daga yarjejeniyar da aka cimma bayan da aka lallami Iran kan ta takaita shirin nukiliyarta, inda daga bisani kasashen duniya suka janye akasarin takunkumin tattalin arzikin da aka sanya wa kasar.

Amman bayan soma jan ragamar mulki, shugaban na Amirka ya soma sukar Iran, inda ya ce ba ta cika wasu daga cikin alkawuran da ta dauka ba, abin da ya sa yake son janye goyon bayan kasarsa. Amirka ta shiga yarjejeniyar karkashin mulkin Barack Obama.

 A watan Yuli na shekarar 2015, Iran da kasashen Jamus da Faransa da Britaniya da Chana da Rasha da kuma Amirkan suka rattaba hannu kan yarjejeniyar takaita shirin nukiliyar.

Illar daukar matakin na Trump ita ce hadarin shiga yaki a yankin Gabas ta Tsakiya mai fama da tashe-tashen hankula.