1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sabon babi a rikicin Amurka da Iran

Zainab Mohammed Abubakar
September 20, 2019

Amurka ta yi martani da sabbin takunkumin tattalin arziki kan Iran a kan zarginta da hannu a harin da aka kai wa masana'antun Saudi Arabiya

https://p.dw.com/p/3PyDw
Bildkombo Donald Trump und Hassan Rohani
Hoto: Getty Images/AFP/N. Kamm//A. Kenare

Shugaba Donald Trump na Amurka ya sanar da sake makawa babban bankin Iran sabbin takunkumi, wadanda ya kira" Takunkumi mafi girma da Amurka ta taba kakabawa wata kasa ta ketare".

Tun a farkon wannan makon nedai shugaban na Amurka ya ce zai dauki matakin kakabawa Tehran sabbin takunkumi, a matsayin abunda jami'an kasar suka ce "martanin Washington" kan hannun Iran din a harin da aka kaiwa masana'antun man Saudi Arabiya.

A cewar shugaban na Amurka dai takunkumin zasu fi aiki fiye da amfani da karfin soji a kan Tehran.