1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Afghanistan: Dakatar da fadan Taliban

Ahmed Salisu
August 19, 2018

Shugaban Afghanistan Ashraf Ghani ya bayyana cewar gwamnatinsa ta amince da wani shiri na wucin gadi na tsagaita wuta tsakaninsa da Taliban na tsawo watanni uku.

https://p.dw.com/p/33Oef
Afghanistan, Kabul: Präsidentenwahl für 2019 angekündigt: Präsident Ashraf Ghani
Hoto: Getty Images/AFP/W. Kohsar

Shugaban ya ambata hakan ne a wani jawabi da ya yi wanda aka yada shi ta gidan talabijin din kasar inda ya ke cewar shirin tsagaita wutar zai fara ne daga Litinin 20 ga wannan watan na Agusta da muke ciki zuwa ranar Talata 20 ga watan Nuwamban da ke tafe.

Baya ga batun tsagaita wutar, Shugaba Ghani ya bukaci 'yan kungiyar ta Taliban da su yi amfani da wannan lokaci wajen hawa kan teburin sulhu da hukumomin kasar don kawo karshen rikicin da suke yi. Ya zuwa yanzu dai Taliban din ba su kai ga cewa komai ba kan hakan. Wannan dai shi ne karo na biyu da gwamnatin ta Afghanistan ke shiga irin wannan yarjejeniya da kungiyar gabannin bukukuwan babbar sallah.