1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

An fara sassauta yaki a Gaza

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim AH
November 24, 2023

Yarjejeniyar dakatar barin wuta na wushin gadi tsawon kwanaki hudu a zirin Gaza don shigar da kayan agaji, ya fara da musanyar fursunonin Falasdinawa 150 da fursunoni Gaza guda 50 da ke hannun sojojin Isra'ila.

https://p.dw.com/p/4ZOCJ
Wani bangare na barnar yakin Isra'ila da Hamas a GazaHoto: Adel Hana/AP/picture alliance

Bayan shafe sama da wata guda na luguden wuta a Gaza tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hamas, yarjejeniyar ba da damar shigo da kayan agaji ya fara aiki a matakin farko.

Kungiyar Hamas da kasashen yammacin duniya suka ayyana a matsayin kungiyar ta'adda za ta sako 'yan Isra'ila guda 50 cikin mutane 240 da ta yi garkuwa da su tun bayan fara yakin. A nata banagaren Isra'ila za ta sako Falasdinawa 150 da ke rike da su. Karin bayani:Sabanin bayanai kan tsare ma'aikatan al-Shifa na Gaza

Gwamnatin Qatar ce ta shiga a madadin kungiyar Hamas wajen cimma wannan yarjejeniyar musanyar fursunoni don tsagaita wuta, bayan tattaunawar kai tsaye da kasar Amirka da kuma Masar.

karin bayani:Isra'ila ta ce babu batun sakin fursunoni kafin ranar Juma'a

Ana sa ran yarjejeniyar za ta tsawaita zuwa kwanaki 10. Ya zuwa yanzu an kiyasta mutuwar Falasdinawa 13,300, da kuma Isra'ilawa 1,400, tun bayan fara yakin a ranar 7 ga watan Oktoban 2022.