1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Gaza: Tsagaita wuta zai fara aiki da karfe 5 safiyar Juma'a

Zainab Mohammed Abubakar
November 23, 2023

A ranar Juma'a (24.11.2023) ne za a fara tsagaita wuta na kwanaki hudu a yakin Isra'ila da Hamas a Gaza, kuma za a yi musayar wadanda ake garkuwa da su da fursunoni bayan sa'o'i kadan.

https://p.dw.com/p/4ZNej
Hoto: Ismail Muhammad/UPI Photo via Newscom picture alliance

Bisa ga shiga tsakaninQatarne aka amince da tsagaita wuta, tare da taimakon Masar da Amurka, wanda ya kamata ya fara aiki tun a wannan Alhamis amma aka samu tsaiko.

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Qatar Majed Al Ansari ya ce, zaa fara tsagaita wutan ne daga karfe 7:00 (:00 GMT)na safe a gobe Juma'a. Kuma za a mika rukunin farko nafarar hulada aka yi garkuwa da su da misalin karfe 4:00 na yamma.

Ya shaidawa manema labarai a Doha cewar, mutane 13 ne za a fara sakewa, dukkansu mata da yara daga iyalai daya. Hakazalika za a saki fursunonin Falasdinawa da ake tsare da su a gidajen yarin Isra'ila, ba tare da bayyana adadinsu ba.