1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin EU da Ukraine

October 18, 2011

EU ta ɗage taron da za ta gudanar da shugaban Ukraine Yanukovyc domin nuna ɓacin ranta game da ɗaure tsofuwar firaministan ƙasar Julia Tymochenko da kotu ta yi bisa angizon shugaban ƙasar.

https://p.dw.com/p/12uNX
Shugaba Yanukovych na Ukraine da sakataren zartaswa na EU BarrosoHoto: AP

Ƙungiyar Gamayyar Turai ta bayyana cewa ta ɗage taron da ta ke da niyar gudanarwa da shugaba Viktor Yanukovych na Ukraine, sakamakon tsamin dangantaka da akae fiskanta tsakanin sassan biyu bayan ɗaure tsofuwar firaminista Julia Tymoshenko da kotun ƙasarsa ta yi. Wata jami'a da ke magana da yawun kantoma Catherine Ashton da ke kula da manufofin ƙetare na Eu, ta ce gamayyar ta ɗauki wannan mataki ne domin jadadda bukatar da ke akwai a Ukraine na daina tsoma bakin shugabannin a harkokin da suka shafi shari'a.

Ita dai EU ta yi Allah wadai da yanke wa tsofuwar firaminista Tymoshenko hukuncin shekaru bakwai a gidan yari da aka yi, saboda a cewarta rawar da shugaba Yanukovych ya taka wajen ɗaure ta. Ita dai ƙasar ta ukraine ta na fatan rattaɓa hannu akan yarjejeniya ƙawance da EU a lokacin wani taron da za a gudanar a birnin Kiev a watan disemba, wanda ke zama matakin farko ga Ukraine na samun kujera a cikin ƙungiyar ta gamayyar Turai.

Mawallafi: Mouhamadou Awal
Edita: Mohammad Nasiru Awal