1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Mexico da Amurka

Abdullahi Tanko Bala
August 28, 2024

Mexico ta dakatar da hulda da Amurka da Kanada kan shirin garanbawul ga fannin shari'a

https://p.dw.com/p/4jzdr
Mexico | Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador,
Mexico | Shugaba Andres Manuel Lopez Obrador,Hoto: Luis Barron/Eyepix Group/NurPhoto/picture alliance

Gwamnatin Mexico ta dakatar da hulda da Jakadun Amurka da Kanada kamar yadda shugaban kasar Andres Manuel Lopez Obrador ya sanar.

Matakin ya biyo bayan katsaladan da Mexico ta ce jakadun sun yi mata kan shirinta na garambawul ga fannin shari'a.

Da yake jawabi ga taron manema labarai Lopez Obrador ya ce sun dakatar da hulda ne da ofisoshin jakadanci amma ba da kasashen ba.

Shirin garanbawul din da shugaban ya gabatar yayin da ya rage yan makonni ya kammala wa'adin mulkinsa ya haifar da zanga zanga da kakkausar suka daga masu zuba jari da kuma cibiyoyin hada hadar kudade.