Tsamin dangantakar siyasa a Nijar
January 6, 2015Talla
A baya-bayan nan dai 'yan adawar kasar sun dauki matakan kauracewa duk wani goron gayyatar da bangaren masu mulki ya yi musu, saboda dalilai na siyasa.
To sai dai a nata bangare, jam'iyyar PNDS tarayya dake mulki na mai ganin rashin abun fadi ne kawai ke ga 'yan adawar. Wannan lamari na faruwa ne a yayin da ake shirin tunkarar zabubbuka a kasar a shekara ta 2016 mai gabatowa.
Tsamin dangantakar dai ya faro ne tun lokacin da masu adawa a Nijar din suka zargi bangaren mulkin da rashin iya jagoranci da cin hanci da rashawa da yin almundahana da dukiyar kasa har da kokarin wargaza jam'iyyun adawa a kasar da nufin ci gaba da kasancewa a kan mulki.
Abdoulaye Mamane Amadou