Diflomasiyya ta yi tsami tsakanin Jamus da Rasha
May 31, 2023Talla
Gwamnatin Jamus ta yanke shawarar rufe hudu daga cikin kananan ofisoshin jakadancin Rasha biyar da ke kasarta, a matsayin ramuwar gayya kan mataki diflomasiyya makamancin wannan da Moscow ta dauka a kanta.
A lokacin da yake bayani a birnin Berlin a kan wannan batu, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Jamus ya shaidawa taron manema labarai cewar, wannan mataki ne na rama wa kura aniyarta.
Baya ga haka a watan Nowamba mai zuwa Jamus din za ta rufe kananan ofisoshin jakadancinta da ke kasar Rasha da suka hadar da na biranen Kaliningrad da Ekaterinbourg da kuma Novossibirsk.