Tsananin zafi da yawon bude idanu
Tsananin zafi da wutar daji da kafewar koguna da karancin saukar ruwan sama: Illar sauyin yanayi na matukar tasiri ga yawon bude idanu a yankunan Turai da suka fi karbar baki.
Spain
Yankin ya bushe, kyallin wuta kadan ka iya tayar da gobara. Spain ta fuskanci gobarar daji mafi muni a tarihi. A biranen Valencia da Alicante da Murcia, jami'an kashe gobara na aiki ba kakkautawa. An kwashe dubban mazauna yankin da masu yawon bude idanu. Abin ya fi kamari a yankunan Andalus na kudancin Catalonia da Aragon a Arewa maso Gabashi da suke da tasiri ga masu yawon bude idanu.
Faransa
A Faransa ma fari ya kai makura a tarihi. Wutar daji ta afku a kasar baki daya har da yankin Gironde da ke gabar teku da kuma ke karbar bakuncin masu yawon bude idanu. Tantuna sun kone, an kwashe dubban masu yawon bude idanu tare da rufe manyan tituna. Fitaccen gandun dajin da ke Dune de Pilat kusa da Arcachon mai shekaru 1,000, na daga cikin yankunan da suka kone.
Potugal
Masu yawon bude idanu na tururuwa zuwa Algarve. Suna samun wadataccen ruwa da wuraren linkaya a otal-otal. Portugal na samun kudin shiga daga masu yawon bude idanu, sai dai akwai rudani saboda tsananin fari da karancin ruwan sama. Ana tunanin otal-otal a Algarve za su rage ruwan da suke facaka da shi. Ko ta ya ya? Wannan ita ce tambayar. A yanzu masu yawon bude idanu na ci gaba da facaka da ruwan.
Ostiriya
Da yanayin zafi da ya haura digiri 39 a ma'aunin Celsius, masu yawon bude idanu a birnin Vienna na jin dadin sanyaya jikinsu a wuraren da aka samar. Guda daga cikin yankuna mafiya kyawun yanayi a Turai, na fama da illar sauyin yanayi da ta haifar da tsananin zafi. Birnin ya samar da tsarin da ya hadar da sakin ruwa da ke fitar da raba domin sanyaya jiki da wurin shan ruwa da ma karin bishiyoyi.
Girka
Tashin hankali a yankunan da ke kusa da birnin Athens da Tsibiran Crete da Lesbos da masu yawon bude idanu ke tururuwa. Wutar daji a Lesbos ta yadu zuwa wurin shakatawa na Vatera a karshen watan Yulin da ya gabata. Mutane sun nemi mafaka a gabar ruwa, inda jami'an tsaron gabar teku suka ceto su. Har yanzu akwai barazana a yankin, akwai sauran tafiya ga Girka kafin lokacin wutar dajin ya wuce.
Holland
A birnin Amsterdam, mutane na dafifi a gabar teku ko Kogin Amstel domin tserewa tsananin zafi. Sai dai a Holland ma fari na janyo matsaloli ga koguna. Ruwan cikinsu na janyewa kana ruwan teku na shiga magudanan ruwa. Babban abin damuwar ma shi ne: Kandagarkin da ke kare kaso 60 na fadin kasar daga ambaliyar ruwa na fuskantar barazana sakamakon kanfar ruwan sama.
Italiya
Tsanain zafi na lalata yanayin kasa. Guda dagaa cikin yankuna mafi karbar masu yawon bude idanu a arewacin Italiya wato Tafkin Garda, na fuskantar janyewar ruwa mafi muni cikin shekaru 15. Duwatsu na fitowa a Tsibirin Sirmione. Masu yawon bude idanu ba sa gane wajen hutawa a gabar teku da wuraren wanka. Jami'an kula da yawon bude idanu sun jaddada cewa za a iya zuwa hutu. Amma za a samu sakewa?
Switzerland
An samar da kandagarkin dusar kankara a baara. Karon farko cikin shekaru 2,000 kusan babu kankara a Col de Zanfleuron da ke yankin Glacier 3000 da ake zamiyar kankara. Masana kan dusar kankara na hasashen zuwa karshen watan Satumba duwatsu za su mamaye wurin. A shekara ta 2012 dusar kankara ta kai mita 15 a wajen. Kankarar da ta narke, za ta zama tafki a yankin da ake wasannin zamiyar kankara.
Birtaniya
Nan London ne? Wuraren shakatawa sun kasance a bushe cikin kura, sun zama ruwan dorawa maimakon kore. Akwai karancin mutane a wuraren cikin birane sakamkon tsananin zafi da ya kai digiri 40 a ma'aunin celsius tun watan Yuli. Ingila ta sanya dokar ta-baci saboda yanayi da kuma kan fari a watan Agusta a yankuna da dama na kasar. Ba a yadda da yin linkaya da ban ruwa da kuma wankin motoci ba.
Jamus
Yankin tsakiyar Kogin Rhine, guda cikin wuraren tarihi na duniya da UNESCO ta ware na karbar baki. Kogin na Rhine ya ja baya zuwa kasa da inci 16 a wasu yankunan. Jiragen ruwan dakon kaya sun rage yawan kayan da suke dauka, an rage na fasinja tare da dakatar da kananan jiragen ruwa. An soke tafiya ta ruwa, abin da ya tilasta mazauna da masu ziyara komawa inda suka fito.