Deby ya cika shekara daya da rasuwa
April 20, 2022Dan marigayi Deby wato Janar Mahamat Idriss Deby Itno mai shekaru 38 da haihuwa ya kwace mulki da taimakon hafsoshin sojojin Chadi, yana mai cewa zai dora inda mahaifinsa wanda ya shafe shekaru 30 a kujerar mulki ya tsaya. Dama dai jim kadan kafin rasuwarsa, Idriss Deby Itano ya lashe zaben da ya ba shi damar tsawaita wa'adin mulkinsa. Hasali ma kasashen Yamma sun dade suna daukar Deby a matsayin mai karfin fada a ji a yakin Sahel da 'yan ta'adda ke addaba da hare-hare, don haka aka dauki dansa a matsayin wanda zai ci gaba da sa kafar wando guda da masu fafutuka da makamai. Gwamnatin rikon kwarya ta mulkin soja a karkashin Janar Deby ta yi alkawari a bara cewa za ta mayar da Chadi kan tafarkin dimokuradiyya ta hanyar gudanar da zabe cikin watanni 18. Amma a daidai lokacin da wannan wa'adin ke dada gabatowa, manazarta da dama na fargabar cewa kasar ba za ta iya mutunta wannan alkawari ba.
Babu wani muhimmin ci gaban da aka samu bayan mutuwar Deby
Adib Saani, wani mai sharhi kan harkokin tsaro na cibiyar kula da harkokin tsaro da zaman lafiya ta Jatikay a Accra babban birnin Ghana ya bayyana cewa babu wani muhimmin ci gaban da aka samu tun bayan da Janar Mahamat Deby ya karbi ragamar mulki."A fili yake cewa babu wani abin kirki da ya sauya a Chadi.
Har yanzu ana fuskantar matsalolin 'yan bindiga, kuma har yanzu rashin tsaro shi ne babbar matsala a wannan yanki. Abin damuwa ma shi ne yadda ayyukan ta'addanci ke yaduwa a wajen kasar, musamman a kasashe makwabta. Wannan na barazana ga kwanciyar hankali a yankin yammacin Afirka."
'Yan adawar na shakku ko sojojin za su mika mulki cikin hannu farar hula
Lokacin da Janar Mahamat Deby ya sanar da shirin kafa gwamnatin soja mai mambobi 15 a cikin watan Afrilun bara, bai dau lokaci mai tsawo wajen fara fuskantar kalubale ba. Da farko dai gwamnatin mulkin sojan na fuskantar matsala wajen cimma matsaya da 'yan tawaye, wadanda suka haddasa mutuwar mahaifinsa. ko da tattaunawar da kungiyoyin 'yan tawaye a birnin Doha na kasar Qatar, wadda aka fara tun ranar 13 ga watan Maris, ba ta haifar da wani sakamako mai ma'ana ba: 'Yan tawayen Chadi da wakilan gwamnatin mulkin sojan kasar sun ki fuskantar juna a duk tsawon lokacin da aka gudanar da shawarwarin. Amma duk da irin wannan tsaiko da ake samu, gwamnatin mulkin sojan Chadi ta ce tana fatan gudanar da wani taron kasa a ranar 10 ga watan Mayu wanda zai share hanyar komawa ga mulkin farar hula. Wannan tsari dai na cin karo da barazana, inda har yanzu 'yan tawaye ke nuna shakku ga gwamnatin mulkin soji yayin da 'yan adawar siyasar Chadi ke barazanar kauracewa taron, lamarin da ke kara dagula al'amura a Chadi.
Sai an tattauna tsakanin 'yan siyasar kasar don samun sulhu
Adib Saani na cibiyar kula da harkokin tsaro da zaman lafiya ta Jatikay ya ce, ba za a iya samun dawwamammiyar hanyar warware rikicin kasar Chadi ba, ko kuma komawa kan mulkin farar hula ba, matikar bangarorin da abin ya shafa masu adawa da juna ba su amince da yin sulhu ba."
Wannan ya danganta da abubuwa da dama, daya daga ciki shi ne tattaunawa, na biyu ne matsin lamba daga kasashen duniya musamman ma Faransa, na uku shi ne matakan da ya kamata a dauka domin zabe ya gudana lafiya. Sai kuma sasantawa tsakanin da Allah, idan bangarori dabam-dabam na hana ruwa gudu, sai ya zama bata lokaci ne kawai. 'Yan adawa 250 da jami'an gwamnati ne ke tattaunawa tun a watan da ya gabata. Daga cikin abubuwan da suke nema shi ne Janar Mahamt Deby ba zai tsaya takara ba a lokacin da za a mayar da kasar ga mulkin farar hula. Sai dai Adib Saani ya ce da kamar wuy" Tsorona shi ne ko da an gudanar da zabe, Déby zai iya tsayawa kuma zai yi nasara kai tsaye, kuma a bisa ka'ida zai kira kansa a matsayin zababben shugaban kasa. A ganina ba wani abu sabo da za a samar daga salon mulkin da deby da dansa ke gudanarwa saboda akwai muradun da suke neman karewa."
Sai dai matsalolin kasar Chadi sun wuce batun komawa kan tafarkin dimokuradiyya kawai ganin cewa barazanar 'yan tawaye da 'yan ta'adda a yankin Sahel na ci gaba da yin kamari; a cewar Majalisar Dinkin Duniya, wasu 'yan kasar Chadi miliyan 5.5 na bukatar agajin gaggawa. Bankin Duniya ya ce kashi 42% na al'ummar kasar miliyan 16 na fama da talauci. A cewar kididdigar ci gaban bil Adama ta Majalisar Dinkin Duniya dai, Chadi ita ce kasa ta uku mafi talauci a duniya mafi talauci.