Tsaune tsayen siyasa bata kare ba a Pakistan
October 20, 2007Talla
A pakistan daruruwan magoya bayan tsohuwar faraminista, Benazir Bhutto, sun gudanar da zanga zangar nuna adawa da harin da aka kai mata.Masu zanga zangar, sun kuma daddatse hanyoyi tare da kone konen tayoyi a ada yawa daga cikin birane a Pakistan din. A lokacin zanga zangar, mutanen sun kuma rera wakokin adawa da gwamnati. A dai ranar alhamis data gabata ne, aka kaiwa tsohuwar faraministar tagwayen hare hare a cincirin don magoya bayan ta a Karachi.Harin ya haifar da rasuwar mutane sama da 140,a hannu daya kuma da jikkata wasu kusan 250. Ya zuwa yanzu dai ana zargin cewa da hannun kungiyoyin yan Taliban da Alqeda a cikin wannan hari.