EU ta tsawaita takunkumi kan Rasha
December 16, 2016Talla
Kungiyar kasashen Tarayyar Turai EU ta amince da shirin tsawaita takunkunmin da suka kakaba wa Rasha saboda mamaye yankin Kirimiya da ke gabashin Ukraine, a yayin taron kungiyar da ya gudana a birnin Brussels na Belgium. Za a ci gaba da aiki da takunkumin kan bangorin tsaro da makamashi gami da tattalin arzikin kasar ta Rasha har zuwa watan Yulin shekara ta 2017.
Shugabannin sun dauki wannan matakin ne sakamakon abin da suka kira yadda kasar ta Rasha take jan kafa wajen aiwatar da yarjejeniyar da ta kulla da Tarayyar Turan kan shawo kan rikicin gabashin Ukraine din. Amma takunkumi bai kunshi matakin Rasha na goyon bayan gwamnatin Shugaba Bashar al-Assad da kasashen Yammaci suke zargi da kama karya ba.