1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsgaita wuta a birnin Aleppo na Siriya

Suleiman BabayoMay 5, 2016

Kasashen Amirka ta Rasha sun amince da matsaya kan shirin tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyu a birnin Aleppo na Siriya.

https://p.dw.com/p/1IiZH
Syrien Zerstörung nach Luftangriff auf Aleppo
Hoto: Reuters/Sana

Gwamnatin Siriya ta amince da tsagaita wuta na tsawon kwanaki biyu a birnin Aleppo da yaki ya dai-daita bayan wata yarjejeniya tsakanin kasashen Rasha da Amirka. Amma duk da haka akwai kara na makamai tsakanin dakarun gwamnati da na 'yan adawa.

Sakataren harkokin wajen Amirka John Kerry ya yi maraba da shirin tsagaita wutar sannan ya bukaci sauran bangarorin su mutunta.

Tsakanin ranakun Litinin da Talata mayakan 'yan tawaye sun harba rokoki kimanin 65 cikin yankin da ke hannun dakarun gwamnati, a cewar kamfanin dillancin labaran gwamnatin kasar. A wani labarin, gwamnatin Jamus za ta karbi bakuncin tattaunawar wakilan 'yan adawa na Siriya yayin da Majalisar Dinkin Duniya ke neman hanyoyin samar da zaman lafiya a kasar ta Siriya.