Tsohon shugaban kasar Aljeriya ya rasu
September 18, 2021Marigayi tsohon shugaban Aljeriya, Abdoulaziz Bouteflika, wanda shi ne ya fi dadewa a kan karagar mulki a Aljeriya, ya mutu ne a ranar Juma'a kamar yadda hukumomin kasar suka tabbatar.
Ya jagoranci kasar na wa'adi hudu daban-daban, da ya kai shekaru 20 na tsawon mulkinsa.
Albdoulaziz Bouteflika ya fuskanci bore daga 'yan kasar wanda ya tilasta masa sauka daga mulki a 2019, saboda kokarin da ya yi na neman zarcewa karo na biyar.
A shekara ta 2011 ma dai marigayin marigayin shugaban na Aljeriya wanda dan darikar Qadiriyya ne, ya fuskanci wani gagarumin bore, sai dai ya sha a lokacin.
Shugabannin kasashen yamma sun yaba kokarinsa wajen yaki da 'yan bindiga inda ke nuna yarda da manufofinsa na yaki da ta'addanci.
Abdozulaziz Bouteflika ya yi fama da shanyewar barin jiki tun cikin shekara ta 2013, cutar da ta hana shi iya fitowa bainar jama'a na tsawon lokaci.