1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban kasar Faransa sai gurfana gaban shari'a

Zulaiha Abubakar
March 30, 2018

Masu gabatar da kara a kasar Faransa sun ba da umarnin Tsohon shugaban kasar Nicolas Sarkozy ya gurfana gaban shari'a sakamakon zargin sa da cin hanci da kuma neman wasu bayanan binciken shari'a.

https://p.dw.com/p/2vEId
Nicolas Sarkozy Archiv 2009
Hoto: Gerard Cerles/AFP/Getty Images

Masu gabatar da karar sun kara da ba da shawarar a gurfanar da lauyansa Thierry Herzog da kuma tsohon Alkali Gilbert Azibert a kan wata shari'a da aka gudanar tun a shekara ta 2014, in dai wannan zargi ya tabbata akan Sarkozy,wannan shi ne karo na biyu da aka tuhumeshi bayan zargin karkatar da kudaden kasar don yakin neman zaben sa a shekara ta 2012.Tsohon shugaban kasar Nocolas Sarkozy mai shekaru 63 ya na fuskantar zargin cin hanci da ya hada da tsohon shugaban kasar Libiya. A nasa bangaren Sarkozy ya bayyana wadannan zarge-zarge da ake masa da cewar karyane da kuma yarfen siyasa.

 

 

      T