Tsohon shugaban Masar Morsi ya rasu a kotu
June 17, 2019Morsi ya rasu a wannanLitinin a wani asibiti a birnin Alkahira inda aka garzaya da shi bayan da ya suma yayin da yake bada bahasi a gaban kotu a cewar majoyin kotu da kuma jami'an tsaro.
Gidan talabijin din kasar ya ruwaito cewa Morsi mai shekaru 67 a duniya ya baiyana a gaban kotu a shari'ar da ake masa ta leken asirin kasa inda ya sami tsawon minti 20 yana jawabi yayin da ya yanke jiki ya fadi. An ruga da shi asibiti inda kuma daga bisani ya rasu.
Morsi wanda dan babbar kungiyar yan uwa musulmi ne na Masar da aka haramta ya kasance shugaban kasar na farko wanda aka zaba bisa tafarkin dimokuradiyya a shekarar 2012 bayan da aka kawar da shugaba Hosni Murabak da ya dade akan karagar mulki.
Sojojin sun hambarar da Mohammed Morsi a shekarar 2013 bayan gagarumar zanga zanga da kuma murkushe 'yan kungiyar 'yan uwa musulmi a wani dirar mikiya tare da kame Morsin da wasu manyan shugabannin kungiyar.