Tsokacin Ostareliya kan sakamakon binciken jirgin MH17
October 14, 2015Talla
A wannan Laraba ce dai hukumomin kasar ta Ostreliya suka ce ba za su amince da duk wani ban tsoro ba, a daidai lokacin da suke neman hakkoki mutanansu daga shari'a. Daga cikin Fasinjojin jirgin 298 da suka rasu yayin wannan hadari dai, 38 dukanninsu 'yan kasar ta Ostreliya ne ko kuma suna zama a kasar. Duk dai da cewa sakamakon bai nuna wanda ke da alhakin kakkabo jirgin ba, amma kuma hukumomin kasar Ukraine da ma kasashen yamma, na zargin 'yan tawayan gabashin kasar ta Ukraine masu goyon bayan Rasha da aikata wannan laifi, zargin da tuni Rasha ta yi watsi da shi, inda ta dora alhakin hakan ga hukumomin Ukraine.