Tsugune ba ta kare ba a Gabon
September 6, 2016Archbishop na Libreville babban birnin kasar ta Gabon, ya bukaci bangaren gwamnati da na 'yan adawa da su kaucewa kara fadada tashe-tashen hankula a kasar. Iyalai da dama sun shiga halin kunci na bacewa ko ma macewar 'yan uwanasu abin da ke zaman wanda ba za su taba mantawa da shi a tarihinsu ba.
A hukumance dai sun bayar da adadin wadanda suka mutu a matsayin mutane bakwai, kana sun sanar da cafke mutane 1,100. Sai dai a ta bakin wani mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Marc Ona adadin wadanda suka mutun dama wadanda suka bace sun fi haka. A ta bakin sakatare janar na jam'iyyar Ali Bongo mai mulki, Faustin Boukoubi 'yan adawa na da damar bayyana ra'ayinsu sai dai ya zama wajibi su girmama doka.
A cewar Mathilde Debain da ke sharhi kan al'amuran siyasa a Faransa, a yanzu haka mutane da dama na cigiyar 'yan uwansu tun bayan da sojojin gwamnati suka kai farmaki a cibiyar yakin neman zaben dan takarar jam'iyyar adawa Jean Ping a Libreville babban birnin kasar.
Tun dai bayan sanar da sakamakon zaben shugaban kasar ne gwamnatin Shugaba Ali Bongo ta toshe hanyoyin sadarwa na Internet, ko da yake an bude jim kadan bayan da lamirin ya sha suka daga kungiyoyin kasa da kasa da Majalisar Dinkin Duniya sai dai ba a iya amfani da kafofin sadarwa na zamani. A cewar Debain koda gidajen talabijin din ksar ma ba sa iya gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, kuma tsahon kwanaki biyar babu wanda ya san me ke faruwa a Gabon.