1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ukraine na zargin Rasha da kokarin mamaye gabashinta

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 5, 2015

Shugaban kasar Ukraine Petro Poroshenko ya sanar da cewa Rasha na kokarin kwace iko da yankin gabashin kasarsa.

https://p.dw.com/p/1FcPM
Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya cika shekara guda a mulki
Shugaban Ukraine Petro Poroshenko ya cika shekara guda a mulkiHoto: picture-alliance/dpa/R. Pilipey

Poroshenko ya bayyana haka ne yayin taron manema labarai da ya gudanar a bikin cikar sa shekara guda a kan karagar mulkin Ukraine din, inda ya ce bai ga dadlilin ci gaba da karya ka'idojin yarjejeniyar tsagaita wutar da suka cimma ba in har ba Rasha na son mamaye yankin gabashin kasar ba ne. 'Yan awaren gabashin Uktraine din dai na goyon bayan mahukuntan Moscow kuma suna da karfin iko a yankin. Cikin wannan makon dai an fuskanci fafatwa mafi muni tsakanin dakarun gwamnatin Kiev da kuma 'yan awaren gabashin kasar da ke goyon bayan Rasha duk kuwa da yarjejeniyar tsagaita wutar da aka cimma tsakanin bangarorin biyu a birnin Minsk.