Tsugune ba ta kare ba a rikicin Libiya
April 5, 2019Duk da cewa dakarun sojan da ke biyayya ga gwamnatin hadin kan kasa da duniya ke amincewa da ita, sun yi kokarin hana dakarun na Haftar kutsawa cikin birnin na Tripoli, tsugune ba ta kare ba, idan akai la'akari da irin shan alwashin da Haftar din ya yi na kutsawa cikin birnin ko ana ha maza ana ha mata. To sai dai kamar yadda Khalid Mushri, shugaban majalisar dokokin kasar ke yin gargadi ga Janar Haftar din, matakin nasa a fasa kowa ya rasa ne.
Ko da yake kamar yadda kakakin sojin da ke biyyayya ga Haftar, Ahmad Mismari ke dagewa, amfani da karfin tuwo ne kadai zai kawo karshen rikicin Libiyan.
Tuni dai kasashen duniya suka yi ca kan wadannan hare-haren da Haftar din ya fara, adaidai lokacin da ya rage 'yan kwanaki a fara tattaunawa kan batun zabe a kasar.
Sakataren MDD, Antonio Guterres na daga cikin wadanda suka fara nuna damuwa kan wannan sabon yamutsin.
Tuni dai kasashen Amirka da Birtaniya da Italiya su kai tir da wannan matakin, suna masu kira da a koma yadda ake a da.
Suma kasashen Masar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Faransa, da ke zama jiga-jigan da ke tallafa wa Haftar, wadanda kuma aka yi ammanar cewa, ba ta yadda za ayi ya dauki wannan matakin ba da saninsu da lamuninsu ba, suma sun fito gaban 'yan jarida sun yi tir da matakin, lamarin da masharhanta ke wa ganin ihu bayan hari.