Tubabbun yara mayaka sun shiga yaki da corona
Yakin basasa ya sanya yara da yawa cikin yaki a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya. Ga wadanda suka yi nisan kwana suka tsere, a yanzu suna taimakawa a yaki da annoba don kare 'yan uwansu.
Coronavirus: Sabon makiyi
Tarin yara tsofaffin mayaka da 'yan unguwar sun hada kai suna tonon rijiya a unguwar talakawa a Bangui, babban birnin kasar. Wadannan matasan na taimakawa don inganta tsabta a uguwanni cikin tsarin Asusun UNICEF. Tuni suka kammala tunon rijiya da mutane dubu 25 ke amfana da ita. An fara aikin tun gabanin bullar corona, amma yanzu kuma hakan na taimako a yaki da annobar bisa tsabta da ake yi.
Aiki tare don zaman lafiya
Wasu matasa sun hau sama, wasu na juya karfe don tunon rijiya. Shirin yana kuma zama bangaren sauya tunanin tsofaffin mayakan, ana koya musu aiki suna samun kudi bayan tserewa daga tarzoma. Yana kuma karfafa wa jama'a su karbe su. An fara shirin tun 2015, kuma yanzu an mayar da shi aikin taimakon kai da kai wajen yaki da corona a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.
Aiki a cikin chabi
Tsofaffin mayaka biyu suna kwashe tabo. Akwai sama da mutane 3,900 da aka tabbatar suna da coronavirus a kasar, ko da yake akwai karancin yin gwaji, wanda hakan zai sa yawan mutanen da suka kamu ya fi haka. Tonon rijiyar shiri ne da ake saran zai kai ga shimfida bututai a fadin kasar. Kimanin kashi 80 cikin 100 na gidajen kasar basu da kayan tsabtace hannayensu.
Neman yarda da amincewar jama'a
Jama'a ta taru don kallon masu tonon rijiya. Tsofaffin yara mayaka kan fuskanci tsangwama da wariya wanda ke kara basu damar komawa fagen yaki. Tallafin da kan iya sa su karbu wajen jama'a na da matukar mahimmanci, kamar yadda dayansu yace: "Wannan aiki zai iya canza rayuwa ta. Daga karshe na samu kudin batarwa, kuma ina taimaka wa wannan al'umma da kasa ta."
Kasa mai firgitarwa
Wadannan kaburbura ne a gefen garin Bossangoa da ke arewa maso yammacin kasar inda aka binne mutanen da aka hallaka. Bayan gwamman shekaru ana fama da rashin zaman lafiya, yaki ya barke a 2013 lokacin da mayaka akasari Musulmai suka kwace mulkin kasar karkashin kungiyar Séléka, daga bisa suma Kiristoci da sauran kabilu suka kafa kungiyar mayakan 'Anti-Balaka'.
Yarjejeniya mai tangal-tangal
Nan sojojin 'yan tawaye na kungiyar 'FPRC' mai karfin gaske ne a tsaye wurin binciken ababen hawa a arewacin kasar. 'Yan tawaye n ke iko da akasarin kasar duk da yarjejeniyar da gwamnati ta cimma tsakaninta da kungiyyoyin mayaka 14. Duk da haka ana cigaba da samun rashin tsaro. Tashin hankali ya karu a yankin 'yan kwanakinnan, inda abokan gaba ke yakar juna don iko da wuraren hakar ma'adinai.
'Yara ba sojoji bane'
Wani allon UNICEF a gefen hanya a Bossangoa na koakrin wayar da kan mutane wajen hana sa yara aikin soja. Tsakanin shekara ta 2014 zuwa 2019 sama da yara dubu 14 aka sako daga hannun mayakan kungiyoyi daban-daban na kasar, amma ana kiyasin har yanzu akawi yara sama da dubu biyar da ke hannun mayaka a kasar, inda wasu ke fuskantar azabtarwa. Wasu na yaki, wasu na girki ko aikin gadi ko masinja.
Neman ilimi cikin mawuyacin hali
Yaran 'yan gudun hijira kenan a cikin aji a karkashin rumfa ta wucin gadi cikin yankin da 'yan tawaye ke iko da shi a Kaga Bandoro. Yara sama da miliyan guda sun bar gidajensu.Bisa kiyasi yaro daga a cikin yara biyar bai taba zuwa makaranta ba. A yankunan da tashin hankalin ya yi kamari, yara hudu cikin biyar ne basa zuwa makaranta.
Fararen hula na cikin tsaka mai wuya
Dakarun Majalisar Dinkin Duniya na sintiri zuwa sansanin 'yan gudun hijira a yankin Bria da ke hannun 'yan tawaye. Wani allo na yin gargadi ga mayakan bisa kawo makamai. Irin wadannan sansanoni suma kansu suna kara jawo barazanar yaduwar coronavirus.
Juriya cikin yaki
Fararen hula cikin Akori-Kura a yankin da FPRC ke iko da shi a gabashin kasar. Majalisar Dinkin Duniya ta yi ce kasar ba ta shirya ba wajen kare kai daga corona. Yakin tawaye ya kassara wuraren kiwon lafiyar kasar wadanda dama can ba wani inganci suke da shi ba, wanda ya tilastawa jami'an kiwon lafiya tserewa daga kasar. A yanzu haka rabin 'yan kasar sun dogara da agaji na kungiyoyin bada tallafi.
Kokarin samar da zaman lafiya
Mata ne nan ke wucewa ta gefen tankar yakin ta MDD a yankin 'yan tawaye na Kaga Bandoro. Akwai matukar tsoron COVID-19 za ta kawo matsalar tsaro tsakanin al'umma, inda farashin kaya zai tashi kana babu hanyoyi shigo da abinci da sauransu. Yayinda aka tsara yin zaben a watan Disamba, wannan shekara ce mai kalubale ga kasar. Masana na cewa ana iya samun tashin hankali a zaben zagaye na biyu.
Hukunta masu karya doka
Matasa na kwallo a sansanin 'yan gudun hijiran Kaga Bandoro. Akalla an bada rahoton cin zarafin yara 500 a bara kawai. Ana kokarin gabatar da shugabannin 'yan tawaye a kotu, amma cin hanci na kawo cikas ga yin hakan.