Tuddan tsira a wasu yankunan Siriya
May 5, 2017Talla
Wakilin Rasha Alexander Lavrentyev ne ya bayyana wannan matakin kwana guda bayan kasashen Turkiya da Iran sun cimma matsaya a taron tsagaita wuta da aka gudanar tsakanin 'yan tawayen Siriya da bangaren gwamnati a birnin Astana. Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterrers ya yi na'am da wannan mataki, amma ya bukaci a fadada dokar hana jiragen Rasha da Turkiyya kai hare-hare a kan yankunan Idlib da Latakia da Aleppo da kuma Hama da aka kebe a arewacin Siriya. Wannan mataki na zama wani yunkuri na rage tashin hankali da ke sanadiyar rayukan fararen hula, sakamakon yawan kai hare-hare da suka tilasta daruruwan al'umma rabuwa da matsugunansu.