Zargin matuka jirgin ruwa da haddasa mutuwar bakin haure
April 24, 2015Kotun na tuhumar Mohammed Ali Malek da ke da shekaru 27 dan asalin kasar Tunusiya da kuma abokin aikinsa Mahmud Bikhit dan asalin kasar Siriya da ke da shekaru 25 da haddasa afkuwar hadarin. Malek dai ana tuhumarsa ne da yin tukin gan-ganci baya ga yin shaye-shaye a yayin da ya ke tukin. Bikhit kuwa ana zarginsa ne da taimakawa Malek wajen yin safarar mutane, zargin da dukkansu suka musanta suna masu cewa suma fasinjoji ne kuma kudinsu suka biya domin a kawo su Turai. Malek da Bikhit na cikin mutane 28 din da suka samu tsira da ransu inda kawo yanzu aka samu nasarar gano gawarwaki 24 daga cikin sama da 700 din da suka hallaka. Jirgin dai ya yi taho mu gama da wani jirgin ruwan daukar kaya, abunda ya yi sanadiyyar hadarin da aka bayyana da mafi muni tun bayan yakin duniya na biyu.