1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Isra'ila: Tuni da ranar harin Hamas

Mahamud Yaya Azare LM
October 7, 2024

A ranar da Isra'ila ke jimamin cika shekara guda da harin ba-zatan da kungiyar Hamas ta kai musu, ta sha alwashin ganin bayansu da 'yanta wadanda Hamas keci gaba da garkuwa da su.

https://p.dw.com/p/4lVt4
Isra'ila | Shekara Guda | Hari | Ba-zata | Hamas
Shekara guda da harin ba-zata da Hamas ta kai Isra'ilaHoto: Ariel Shalit/AP Photo/picture alliance

Rokokin Hamas sun fada kan birnin Tel Aviv na Isra'ila, a daidai lokacin da suma kungiyoyin Hezbollah na Lebanon da 'yan Huthi na Yemen suma suka harba nasu rokokin. Kungiyar ta Hamas dai ta ce ta harba rokokin ne, domin jaddada aniyarta ta ci gaba da gwagwarmaya a matsayin hanya daya tilo ta 'yanta Falasdinawa daga mamayar Isra'ila. Mummunan martanin da Isra'ila ke kai wa da galibin kasashen duniya ke yin tir da shi bayan ta halaka kimanin mutane dubu 42 a Gaza da wasu dubu uku a Lebaonon, ya janyo maka Isra'ila gaban kotun duniya kan zargin ta da yiwa Falasdinawa kisan kare dangi. Shugaban Faransa Emmanuel Macron dai, ya yi kira ga duniya da ta dakatar da bai wa Isra'ila makamai. A jawabin firaministan Isra'ilan Benjamin Netanjahu na jimamin tunawa da harin na bakwai ga watan Oktoban bara, ya siffanta ranar da tarihi da kuma yin alkawarin ci gaba da kare 'yan Isra'ila daga wadanda ya siffanta da gayyar sharri.