Tunusiya na zaman makokin rasuwar Essebsi
July 25, 2019Marigayin mai shekaru 92 gogaggen dan siyasa ne mai ra’ayin gurguzu da kawo sauyi tun yana matashinsa, yadda gama karatinsa a Faransa ke da wuya a shekarar 1952 ya tsunduma cikin fadi tashin siyasa.
Alakar kut da kut da yake da ita da tsohon shugaban kasar Borgibah, tun daga shekarar 1965 har zuwa 1986 ya daga sunanasa a tarihin siyasar kasar, yadda ya rike mukaman ministan tsaro dana cikin gida da na harkokin waje, da kuma nada shi jakadan kasarsa a Faransa, yadda a wannan lokacin ya cira tuta, bayan da a karon farko yayi nasarar shawo kan kasashen duniya wajen yin Allah wadai da kama wuri zauna da Isra’ila ke yi a yankunan Falasdinawa.
A zamanin mulkin shugaba Zain el Abideen Bin Ali, Essebsyn yayi shekara guda kan shugabancin Majalisa a shekarar 1990, inda aka yi ta kai ruwa rana da shi da fadar shugaban kasa, lamarin da ya kai shi ga yin murabus a jam’iyya mai mulki dama kauracewa siyasa baki daya bayan karewar wa’adinsa na majalisa.
Bayan da guguwar juyin juya hali ta yi awon gaba da mulkin Zain el Abedeen, an nada shi shugaban rikon kwarya da ta shirya zabe da ya sha yabo ciki da wajen kasar.
A shekarar 2014 an zabe shi a matsayin shugaban Tunisiya na farko karkashin tsarin dimokiradiya, ya kuma kafa gwamnatin hadaka da kungiyar Annahdhah ta yan uwa musulmi duk da kiraye kirayen da ake masa ya raba gari dasu, koma ya jerasu cikin kungiyoyin ‘yan ta’adda lamarin da ya sanya Tunusiya ta zama kasa daya tilo da juyin juya hali yayi nasara cikin kasashen larabawa.
An zarge shi da zakewa wajen bawa mata musulmi ‘yancin auren wadanda ba musulmi ba da daidaita su da maza a wajen rabon gado gami da danka igiyar saki a hannunsu.
A tsawon mulkinsa na shekaru hudu ya sha fama da hare haren kungiyoyin ‘yan ta’addan da yai nasarar karya lagonsu, kamar yadda yayi nasarar taka birki ga koma bayan tattalin arzikin da kasar ke fuskanta ta hanyar farfado da kananan masana,antu da bunkasar bangaren yawan shakatawa.
Duk da cewa ya fito karara yace ba zai sake tsayawa takara ba, sai dai masu sukarsa na zarginsa da shirin gadar da kujerar shugabancin kasar ga dansa Hafiz Essebsi, dake zama kusa a jam’iyyar da mahifinnasa ya kafa Nidaa Tunis. Tuni dai aka sanar da kakakin majalisar kasar Muhammad Nasir a matsayin shugaban riko kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.