Zaben 'yan majalisar dokoki a Tunusiya
October 6, 2019Talla
Rahotanni sun nunar da cewa 'yan takara dubu 15 akasari masu zaman kansu, wasu kuma daga wasu kananan jam'iyyun da aka kirkira baya-bayan nan za su fafata domin neman kujeru 217 da majalisar ta kunsa, inda mutane miliyan bakwai da ke da rijistar zabe za su kada kuri'unsu.
Sai dai ana ganin zaben 'yan majalisar ba shi da armashi a idon 'yan kasar ta Tunusiya da dama, kasancewa yana gudana ne tsakanin zagayen farko da na biyu na zaben shugaban kasa, wanda 'yan takara biyu suka bayar da mamamki wato Kais Saeid da kuma Nabil Karuoi wanda yanzu haka yake tsare a gidan kaso ne za su fafata.