1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tura sojojin Sin zuwa Jibuti ya dau hankalin Jaridun Jamus

Mohammad Nasiru Awal
July 14, 2017

A karon farko Chaina ta tura sojojinta zuwa wani sansanin soji a ketare, yanzu haka wani jirgin ruwan yakin kasar na kan hanyar zuwa kasar Jibuti da ke gabashin Afirka, inda kasar za ta kafa wani sansanin soji.

https://p.dw.com/p/2gZPT
China Djibouti Militärbasis
Jirgin ruwan yaki na Chaina a gabar ruwan Jibuti.Hoto: picture alliance/AP/Xinhua News Agencyvia/W. Dengfeng

Kamar dai yadda Chainar ta nunar, za ta rika kula da aikin taimakon jin kai da sojojin duniya karkashin inuwar Majalisar Dinkin Duniya. An kuma yi maganar hadin kan aikin soji da atisayen sojin ruwa da aikin ceto a yankin tekun Aden. Jaridar ta ce kawo yanzu ba a san yawan sojojin da Chainar za ta girke a Jibutin ba, inda tuni kasashen Amirka da Faransa da Italiya da Spaniya da Japan da Turkiyya ke da sojoji. Ita ma kasar Saudiyya ta gina sansanin soji a kasar ta Jibuti da ke a yankin Kahon Afirka.

Daga lokacin zabe a Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ya dauki hankalin jaridar Neue Zürcher Zeitung

Jaridar ta ce, 'yan adawa a kasar ta Jamhuriyar Demokardiyyar Kwango sun bayyana sanarwar da aka bayar cewa ba za a iya gudanar da zaben a wannan shekara da wani abu mai kama da tsokana. A watan Disamban 2016 kungiyoyin adawa da gwamnati suka amince da a gudanar da zaben a karshen shekara ta 2017. Tun a Disamban bara ne kuwa wa'adin shugabancin Joseph Kabila ya kare kuma bisa tsarin mulkin kasar ba zai iya yin takara karo na uku ba. ‘Yan adawa sun ce matakin dage zabe wani kokari ne na bai wa Kabila damar yin mulki na har sai bayan rai. Domin gwamnatin kasar ce ke da alhakin rigingimun da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin na Kasai.

Ba a samu isasshen lokacin tattauna batun taimakon raya kasa ba, wannan shi ne taken labarin da jaridar Süddeutsche Zeitung ta buga a tsokacin da ta yi dangane da taron kungiyar G20 a Jamus, inda aka sa rai za a yi tattaunawa mai tsawo kan  taimakon nahiyar Afirka.

Kamar yadda aka saba Afirka kan kasance kan ajandar manyan taruka, a kullum kuma ana maganar yaki da yunwa da inganta harkar bada ilimi. Haka ma batun ya kasance gabanin taron kolin G20 da ya gudana a birnin Hamburg da ke arewacin Jamus. Mai masaukin baki kuma shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta yi fatan cewa kasashe masu arzikin masana'antu da masu samun bunkasar tattalin arziki su kara daukar nauyin tallafa wa Afirka. Amma a fakaice a karshen taron ta amsa cewa a gaskiya batun taimakon raya kasa bai dauki hankali sosai ba a karshen taron.