Muhimman abubuwan da suke sahun gaba a dangantakar da ke tsakanin kasashen nahiyar Afirka da kuma kungiyar Tarayyar Turan sun hadar da batun samar da zaman lafiya da kasuwanci da zuba jari da ilimi da fannin lafiya da kuma bada tallafi ga kungiyoyin farar hula.