Kamen masu taya Maroko murna a Turai
December 11, 2022Talla
A birnin Paris jami'an tsaro sun tabbatar da tsare mutane 108, inda suka ce sama da mutane dubu 20 ne suka yi tattaki a dandalin Champ-Elysees. Jami'an tsaro sun ce magoya bayan Marokon sun harba musu tartsatsin wuta, yayin da suke kokarin dakatar da su. A biranen Amsterdam da Rotterdam da kuma Utrecht na kasar Holland kuwa, bayan kame wasu mutanen jami'an tsaro sun tabbatar da mayar da doka da oda. A Brussels babban birnin Belgium ma sama da mutane 60 aka tabbatar da damkewa, yayin da a birnin Milan na Italiya aka dabawa wani mutum dan arewacin Afirka wuka a wuya a lokacin bikin nasarar ta Maroko.